Asabar 22 Agusta 2026 - 23:15
Kano: An Gudanar da Zaman Juyayin Shahadar Imam Hassan Al-Askari (AS)

Hauza/ Yan uwa Musulmi almajiran Sheikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H) na birnin Kano sun gudanar da zaman juyayin shahadar Imam Hassan Al-Askari (AS), Imami na goma sha ɗaya daga cikin Ahlul-Baiti (AS).

A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, an gudanar da taron ne a yammacin ranar Juma’a, 21 ga Agusta 2026, wanda ya yi daidai da 8 ga watan Rabi’ul Auwal 1448H, a Hussainiyyar Imam Ridha da ke Kofar Waika, Kano, da misalin ƙarfe 5:00 na yamma.

An fara zaman da waƙoƙin juyayin shahadar Imam Hassan Al-Askari (AS), inda mahalarta suka amsa tare da bugun ƙirji domin tunawa da shahadar Imamin da kuma bayyana alhini da kauna ga Ahlul-Baiti (AS).

Daga bisani, Wakilin ’yan’uwa Musulmi na garin Kano, Shaikh Dr. Sunusi Abdulkadir Koki, ya gabatar da jawabi kan tarihin rayuwar Imam Hassan Al-Askari (AS), tare da bayyana irin matsin lamba da tsanantawar da Imamin ya fuskanta a zamaninsa.

Shaikh Sunusi ya kuma yi bayani kan dalilin da ya sa aka yi wa Imam Hassan Al-Askari (AS) lakabin “Al-Askari”, inda ya bayyana cewa an tsare Imamin a wani sansanin soji, daga nan ne aka danganta sunansa da wannan lakabi.

A wani ɓangare na jawabin, ya bayyana cewa Imam Hassan Al-Askari (AS) ya fuskanci tsanantawa daga azzaluman zamaninsa, kuma daga ƙarshe ya yi shahada sakamakon gubar da aka sanya masa a cikin abinci.

A ƙarshen taron, mahalarta sun karanta Ziyarar Imam Hassan Al-Askari (AS) tare da Ziyarar ɗansa, Imamul Hujjah Al-Mahdi (AJTF).

Daga nan ne aka gudanar da Sallar Magariba da Isha’i, sannan aka rufe taron da addu’a da sallamar mahalarta.

Kano: An Gudanar da Zaman Juyayin Shahadar Imam Hassan Al-Askari (AS)

Kano: An Gudanar da Zaman Juyayin Shahadar Imam Hassan Al-Askari (AS)

Kano: An Gudanar da Zaman Juyayin Shahadar Imam Hassan Al-Askari (AS)

Kano: An Gudanar da Zaman Juyayin Shahadar Imam Hassan Al-Askari (AS)

Kano: An Gudanar da Zaman Juyayin Shahadar Imam Hassan Al-Askari (AS)

Kano: An Gudanar da Zaman Juyayin Shahadar Imam Hassan Al-Askari (AS)

Kano: An Gudanar da Zaman Juyayin Shahadar Imam Hassan Al-Askari (AS)

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha